Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na citifmo online cewa, a cikin makon nan mabiya addinin muslunci a kasar Ghana sun gudanar da wani jerin gwano a sassa na jahar yammacin kasar domin nuna rashin jin dadinsu da amincewarsu dangane da matakan da ake dauka a kansu na hana su gudanar da harkokin addininsu a cikin 'yanci da walwala.
Daga cikin irin matakan da ake dauka na takura musulmi hard a hana mata saka hijabia ckin makarantu, wanda kuma hakan ya yi hannun riga da dokokin da ke cikin kundin tsain mulkin kasar da suka baiwa kowane dan kasa damar gudanar da harkokinsa na addini ba tare da wata tsangwama ba, kuma hijabi na daga cikin muhimman lamurra a cikin addinin muslunci.
Bayan da dalibai da sauran musulmi suka fara gudanar da wannan zanga-zanga ta nuna rashin amincewa da takura dalibaia amakarantu, gwamnatin kasar ta sanar cewa za ta dauki dukaknin matakai na kare hakkokin musulmi, da hakan ya hada da ladabtar da masu takura musu a cikin makarantu saboda saka hijabin muslunci.
Kasar Ghana dai tana da mabiya addinai daban-daban amma mafi yawancinsu mabiya addinin kirista ne, kuma tuni su suka sanar cewa bas u amince da cin zarafin musulmi ba, kuma suna fatan za a warware matsalar saka hijiabin muslmia makarantu ta hanyar lumana, domin al'ummomin kasar suna zaman lafiya.
Kimanin kashi 51% na mutanen kasar suna bin kiristanci ne, sai kuma kashi 21% suna bina ddinin gargajiya, yayin da kashi 20% mabiya addinin muslunci ne.
2886992