IQNA

Kona Majalimia’r Qods Da Yahudawa Suka Ya Kara Tabbatar Da Dabbancinsu

23:41 - February 27, 2015
Lambar Labari: 2906471
Bangaren kasa da kasa, Hana Isa bababn sakaraen cibiyar hada kan musulmi da iristoci ya bayyana cewar a jiya ne wasu yahudawan sahyniya da ke samun kariyar gwamnatin Isra’ila suka kaddamar da hari kan wata majamia a kudancin garin bait Laham kuma suka kone shi kurmus.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cewa, kamar dai yadda suka saba wasu yahudawan sahyniya da ke samun kariyar gwamnatin Isra’ila sun  kaddamar da harin ta’addanci kan wata majami’a mallakin kiristocin palastinu, da ke kudancin garin bait Laham kuma suka kone shi da wuta ba tare da wani y ace da su uffan ba.
Wannan mataki dai wanda ba shi ne na farko ba kuma ba zai zaman a karshe ba, ya zo ne a lokacin da yahudawan masu tsattsauran ra’ayi suke ci gaba da zafafa hare-harensu babu kakkautawa a kna palastinawa musulmi da kuma mabiya addinin kirista ba tare da wani banbanci ba.
Yahudawan Isra’ila dai suna aikata hakan tare da cikakken goyon bayan haramatacciyar gwamnatinsu, da ke basu kariya a kowane lokaci suke aikata irin wannan barna da ta’asa kan palastinawa.
Kasashen da suke raya cewa suna kare hakkokin bil adama  akasashen turai su ne kan gaba wajen mara baya ga irin wadannan ayyuka na ta’addancin Isra’ila kan sauran al’ummomi.
2904391

Abubuwan Da Ya Shafa: Qods
captcha