Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na PressTV cewa, Wata kotu a birnin Alkahira na kasar Masar ta sanya kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas cikin jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda.
Gidan talabijin din gwamnatin Masar ya watsa labarin cewa; Wata kotu a birnin Alkahira na kasar Masar a yau Asabar ta zartar da hukuncin sanya kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas cikin jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda a kasar, kuma wannan mataki ya zo ne bayan kasa da wata guda da sanya bangaren sojin kungiyar cikin jerin ‘yan ta’adda a hukumance.
Wani lauyan kasar Masar mai suna Samir Sabari ne ya shigar da karar kan kungiyar Palasdinawa ta Hamas yana zarginta da hannu a aiwatar da ayyukan ta’addanci a cikin kasar Masar ciki har da fasa gidan kurkuku da kashe masu zanga-zangar lumana a dandalin Tahrir na birnin Alkahira a lokacin shugabancin Muhammad Morsi na kungiyar ‘yan uwa musulmi a shekara ta dubu biyu da sha uku.
A kan hakan daruruwan palastinawa ne magoya bayan kungiyar Hamas da ma wasu kungiyoyin daban suka gudanar da zanga-zanga a cikin yankin zirin Gaza domin nuna rashin amincewa da wannan hukunci na kotun Masar dsa ya saka Hamas a ckin kungiyoyin ‘yan ta’adda, saboda abin da abin da yake faruwa ayankin sina na kasar.