IQNA

Shugaban Kasar Ghana Ya Kare Hakkin Mata Musulmi Dangane Da Saka Hijabi

22:21 - March 04, 2015
Lambar Labari: 2928897
Bangaren kasa da kasa, musulmi mata a kasar Ghana suna gamsuwarsu dangane da kalaman John Mahama shugaban kasar dangane da hakkokin mata na saka hijabi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na AA cewa, furucin na shugaban kasar ta Ghana ya faranta ran mabiya addinin muslunci a kasar.
A cikin makon day a gabata ne mabiya addinin muslunci a kasar Ghana suka gudanar da wani jerin gwano a sassa na jahar yammacin kasar domin nuna rashin jin dadinsu da amincewarsu dangane da matakan da ake dauka a kansu na hana su gudanar da harkokin addininsu a cikin 'yanci.
Irin matakan da ake dauka na takura musulmi hard a hana mata saka hijabia  ckin makarantu, wanda kuma hakan ya yi hannun riga da dokokin da ke cikin kundin tsain mulkin kasar da suka baiwa kowane dan kasa damar gudanar da harkokinsa na addini ba tare da wata tsangwama ba, kuma hijabi na daga cikin muhimman lamurra a cikin addinin muslunci a kasar.
A lokacin da dalibai da sauran musulmi suka fara gudanar da wannan zanga-zanga ta nuna rashin amincewa da takura dalibaia  amakarantu, gwamnatin kasar ta sanar cewa za ta dauki dukaknin matakai na kare hakkokin musulmi, da hakan ya hada da ladabtar da masu takura musu a cikin makarantu saboda saka hijabin muslunci.
Wannan dai tana da mabiya addinai daban-daban  amma mafi yawancinsu mabiya addinin kirista ne, kuma tuni su suka sanar cewa bas u amince da cin zarafin musulmi ba, kuma suna fatan za a warware matsalar saka hijiabin muslmia  makarantu ta hanyar lumana, domin al'ummomin kasar suna zaman lafiya da kowa.
2924477

Abubuwan Da Ya Shafa: ghana
captcha