IQNA

‘Yan Ta’addan Boko Haram Sun Wa Masu Karatun Kur’ani Kisan Kiyashi

15:55 - March 07, 2015
Lambar Labari: 2941593
Bangaren kasa da kasa, yan ta’addan Boko Haram sun yi wa wasu masu karatun kur’ani mai tsarki a garin Goza na arewacin Najeriya kisan kiyashi.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Lesoir.be cewa, ya nakalto daga wani mazaunin garin na Goza cewa, yan Boko Haram sun yi kisan kiyashi a kan wa wasu masu karatun kur’ani mai tsarki a garin.

A nata bangaren rundunar sojin Nijeriya sun sanar da cewa suna ci gaba da samun nasarori a fadar da suka kadddamar kan kungiyar Boko Haram inda suka ce sun sami rumbunan makamai da ‘yan Boko Haram din suka boye bayan kwace garin Baga da suka yi daga hannun ‘yan Boko Haram din a shekaran jiya.

Shi ma kakakin sojojin na Nijeriya cikin wata sanarwa da ya fitar a ya ce sojojin suna ci gaba da gudanar da bincike da kuma kai hare-hare kan maboyar ‘yan ta’addan, inda ya ce sojojin sun samo nau’oi daban-daban na makamai a ci gaba da binciken da suke yi a garin baga na jihar Borno bayan kwace shi daga hannun ‘yan Boko Haram din.

Wasu rahotannin sun ce daya daga cikin aikin da aka dora wa sojojin shi ne kamo shugaban kungiyar Boko haram din Abubakar Shekau wanda a baya sojojin suka ce sun kashe shi amma dai daga dukkan alamu labarin bai tabbata ba.

Gwamnatin Nijeriyan dai ta sanar da cewa cikin makonni shida za ta gama da kungiyar Boko Haram din, wanda shi ne ma dalilin dage zaben kasar da aka yi daga makon da ya wuce zuwa ga karshen wata mai kamawa.

A wata sanarwa da ta fitar, rundunar Sojin kasar ta ce kimanin mayakan boko haram dari da hamsin su kai hari garin na Kondiga tare da taimakon 'yan kato da gora Sojojin sun samu nasarar dakille wannan hari, inda suka hallaka mayakan na Boko haram fiye da saba’in.

Rahoton ya ce an kwashe sa'o'I shida ana tafka gumurzu tsakanin bangarorin biyu, kafin daga bisani mayakan na boko haram da suka tsira da rayukansu suka arce daga garin.

Wani dan kato da gora ya ce sun hallaka mayakan boko haram saba’in da uku, kuma wadanda suka tseran an tayar da wani jirgin yaki daga Maiduguri domin farautar su.

Har ila yau a jiya Litinin jami'an tsaro sun hallaka wani dan kunar bakin wake wanda ya shigo garin na Kondiga cikin Mota shake da bamai- bamai kafin ya tayar da bama-bamai aka bindige shi.

2939246

Abubuwan Da Ya Shafa: najeriya
captcha