IQNA

Ya zama Wajibi A Hada Kai Domin Yaki Da Ta’addanci

22:26 - March 09, 2015
Lambar Labari: 2956497
Bangaren kasa da kasa, Sheikh Ahmad Tayyib babban malamin cibiyar Azahar a lokacin da yake ganawa da Sa’ad Al-hariri ya bayyana cewa, dole ne a hada kai domin shiga kafar wando daya da ‘yan ta’addan da suke barazana ga kowa.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Yaum Sabi cewa, a lokacin ganawar Ahmad Tayyib da kuma Sa’ad Hariri shugaban jam’iyyar Al-Mostaqhbal ta kasar Lebanon ya bayyana wajabcin  hada kai domin shiga kafar wando daya da ‘yan ta’addan da suke barazana ga zamana lafiyar al’ummomin yanin gabas ta tsakiya da ma duniya baki daya.
Jami’ar ta kirkiro wata cibiya  ta yanar gizo a kokarin da take yin a fada da tsaurin ra’ayi na addini da ya fara zama karfen kafa ga kasashen duniya musamman kasashen musulmi, inda ake yaudarar yara matasa musulmi da sunan addini wajen aikata ayyukan ta’addanci a duniya, wanda hakan ke bata sunan wannan addinin mai tsarki.

Yayin da yake sanar da hakan daya daga cikin manyan jami’an Jami’ar ta Azhar ya ce a halin yanzu dai  bisa la’akari  da irin yadda masu tsaurin ra’ayin suke amfani da hanyoyin sadaukar na zamani wajen yada akidunsu don haka ya zama wajibi a kirkiro hanyoyi na zamani wajen fada  da  wannan shiri na  su.

Jami’in ya kara da cewa ta hanyar wannan sabuwar cibiyar za a sami damar wayar da kan mutane kan hakikanin koyarwar Musulunci da kuma rashin ingancin abubuwan da masu tsaurin ra’ayin suke yadawa  da kuma hanyoyin da suke bi wajen janyo hankulan mutane zuwa gare su.
2953163

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha