IQNA

Sojin Isar’ila Sun kai farmaki Kan wani Yaro Palastine aA Cikin Masallacin Qods

23:18 - March 16, 2015
Lambar Labari: 2996921
Bangaren kasa da kasa, sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kaddamar da farmaki a yau kan wani karamin yaro bafalastne a cikin masallacin Qods mai alfarma.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na IMEMC cewa, a yau sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kaddamar da farmaki a yau kan wani karamin yaro bafalastne a cikin masallaci bayan da suka shiga cikinsa dauke da makamai.
Ita kuma a nata bangaren Kotun kasa da kasa mai shari’ar manyan laifuffukan yaki  ta sanar da fara gudanar da bincike kan zargin haramtacciyar kasar Isra’ila da ake yi da tafka laifuffukan yaki a yayin yakin da ta kaddamar kan Zirin Gaza a shekarar da ta gabata.
Babbar mai shigar da kara a kotun ce ta sanar da hakan cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Juma’a inda ta ce za ta gudanar da bincike cikin adalci ba tare da goyon bayan wani bangare ba kan wannan batu.

Fara gudanar da binciken dai ya biyo bayan mika takardun shiga cikin yarjejeniyar kotun ne da hukumar cin gashin kan Palastinawa ta yi a kwanakin baya lamarin da ya ba ta damar kai karar haramtacciyar kasar Isra’ila kotun saboda aika-aikan da take yi a kan al’ummar Palastinu musamman harin da ta kai a kwanakin baya wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dubban palastinawa.

2991611

Abubuwan Da Ya Shafa: Qods
captcha