Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Almanar cewa, Hizbullah ta yi kakausar suka dangane da harin ta'addancin da aka kai a kasar Tuniya tare da bayyana hakan da cewa wannan aiki ne da ke cika burin sahyuniyawa makiya al'ummomin larabawa da musulmi.
Hizbullah ta nuna alhini ga dukkanin wadanda suka rasa danginsu da iyalansu a cikin wannan hari na ta'addanci, tare da bayyana cewa masu aikata bas u wakiltar addinin muslunci, bil hasali ma su makiya ne na dkkanin addinai da aka safkar daga sama, kuma manufarsu ita ce yaki da wadannan addinai da mabiyansu a duniya.
Bayanin na Hizbullah ya kara da cewa ta'addanci bas hi da addini, bil hasali ma masu aikata hakan suna da laka ta musamamn da makiya dukkanin addinai na duniya wato yahudawan sahyuniya wadanda ba su yi imani da wani addini ba hatta addinin yahudanci suna gaba shi da koyarwarsa, wada kuma su ne ked a hannu wajen samar da wadannan yan ta'adda.
Haka nan kuma bayanin ya ja hankulan malamai das u mike wajen fadakar matasa da ake yaudara da sunan addini suna shiga kungiyoyin da ke dauke da akidun kafirta musulmi, wadanda das u ne ak amfani wajen aiwatar da wanann mummunar manufa ta makiya addinin muslunci a duniya.