Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Alalam cewa, dubun dubatan mutanen kasar Yemen sun fito kan tituna babban birnin kasar, San’ah don yin Allah wadai da kuma tofin Allah tsine ga kasar Saudiyya dangane da hare-haren da ta kaddamar kan kasar, suna masu nuna goyon bayansu ga sojojin kasar da kuma dakarun kungiyar Ansarullah da kiransu da su dau fansa wannan harin.
Wannan jerin gwanon dai, wanda kungiyar Ansarullah da sauran kungiyoyin masu goyon bayan juyin juya halin kasar Yemen din suka kira, ya biyo bayan hare-haren da sojojin Saudiyya da na kawayenta suka kaddamar ne kan cibiyoyin kungiyar ta Ansarullah bugu da kari kan wasu filayen jiragen saman kasar da wasu gidajen fararen hula.
Kungiyoyi da ‘yan siyasa na kasashen duniya daban-daban suna ci gaba da Allah wadai da wannan wuce gona da iri na Saudiyyan da suka bayyana shi a matsayin wani kokari na mamaye kasar ta Yemen da Saudiyya take yi da kafa gwamnati ‘yar amshin shatanta a wajen.
Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta yi kakkausar suka da kuma Allah wadai da wannan wuce gona da iri na Saudiyya da Amurka a kan al’ummar Yemen din. Su ma a nasu bangaren al’ummar kasar Bahrain sun sanar da gudanar da wata zanga-zanga nuna goyon bayansu ga al’ummar kasar ta Yemen. Shi kuwa shugaban kwamitin harkokin wajen na majalisar shawarar Musulunci ta Iran Alaudden Burujerdi ya ce ko shakka babu wutar fitinar da Saudiyya ta kunna a kasar Yemen za ta koma kanta.
3042169