IQNA

An Sace Wani Dadadden Kur’ani Mai Shekaru 700 A Kasar India

16:35 - March 28, 2015
Lambar Labari: 3050351
Bangaren kasa da kasa, an sace wani kwafin kur’ani mai tsarki wanda ya jima har tsawon shekaru kimanin 70 a jahar Rajestan ta kasar India.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar NDTV cewa, Jaidu Prasad dan shekaru 55 da haihuwa, shi ne mamallakin wannan kwafi na kur’ani mai tsarki, wanda kuma mabiyin addinin Hindu ne, ya kuma ce ya samu wannan kur’ani ne a cikin shekara ta 2011 kyauta daga wasu abokansa.
Ya ci gaba da cewa wasu daga cikin mutanen da yakan yi harkar kasuwanci tare da su ne suka ce kur’anin, inda wani daga cikin ya shammace shi a lokaci da yake Magana da wayar tarho, ya sa masa makami yana yi masa barazanar kashe shi, ko kuma ya bashi kwafin kur’anin, da haka a karbe shi daga hannunsa.
Ya kara da cewa daya daga cikin abubuwan da ke da muhimamnci danagne da wanann kur’ani shi ne, an rubutunsa ne da ruwan zinari, kuma alamominsa an yi su ne da dutsen yakutu mai daraja, kuma yana niyyar bayar da shi ne kyauta ga matar da yake so.
‘Yan sanda sun ce an sace kur’anin ne saboda kimarsa, da kuma kasancewarsa wani abin tarihi, amma dai suna gudanar da bincike kan lamarin.
3046231

Abubuwan Da Ya Shafa: india
captcha