Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Manarah cewa, a jiya ne aka fara gudanar da zaman taron domin bicike kan ilmomin kur’ani mai tsarki domin kara fitar da wasu abubuwa da suke boye na daga ilimi.
Wannan zaman taro dais hi ne karo na uku da ake gudanar da shi, bayan gudanar da wasu biyu makamantansa a cikin shekarun da suka gabata, inda masana suke gudanar da bahasi kan batutuwan da suka danganci ilmomin kur’ani mai tsarki, da ke bukatar bincike a kansu.
Ana gudanar da taron ne tare da hadin gwaiwa da bababr cibiyar binciken ilmomin addinin mulsunci ta Modei da kuma babban kwamitin malaman kasar ta Morocco, inda dukakninsu suke bayar da gudunmawa dangane da fitar ilmin tafsirin kur’ani wanda ya doru a kan bahasi da kuma dalilan safkar ayoyi.
Taron dai yana samun masana da kuma malamai a bangaren ilmomin kur’ani daga sassa na kasar, kuma ana saran kamala shi gobe tare da fitar da bayani kan abubuwan da aka yi bahasi a kansu wadanda za a buga su a matsayin littafi domin amfanin masu bincike.
3116087