Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alwafd cewa, Muhammad Abdulwazzaq kakakin ma’aikatar harkokin addini a kasar Masar ya bayyana cewa, batutuwa na siyasa ne babban dalilin da yasa ba a gayyaci jamhuriyar muslunci ta Iran zuwa gasar kur’ani ta kasar masar karo na 22, kamar yadda kuma ba a gayyaci kasashen Turkiya da Qatar zuwa wannan gasa ba, saboda matsalolin da ke tsakaninsu da Masar.
Ya ci gaba da cewa Iran tana daya daga cikin kasashen da suke goyon bayan ayyukan ta’addanci a rayawarsa, kuma tana kokarin yada mazhabar italan gidan amnzon Allah a kasar a cikin kasar ta Masar, saboda haka kasar masar ta dauki wanann mataki na kin gayyatar wakilan Iran a wannan gasa.
Duk da irin wannan mataki da kasar Masar take dauka kan jamhuriyar muslunci ta Iran, a nata bangaren Iran tana bayar da muhimamnci matuka wajen gayyatar dukkanin kasashen musulmi a tarukanta na gasar kur’ani da hakan ya hada da wakilan kasar Masar, domin kuwa batu na kur’ani bai dace a saka batun siyasa a cikinsa ba.
Abin takaici ne yadda babban malami mai bayar da fatawa na cibiyar Azhar ya fito karara ya goyi bayan kaddamar da hare-haren ta’addanci na gwamnatin Saudiyya kan al’ummar kasar Yemen, har ma yake bayar da fatawar halascin hakan, inda yake bayyana yan kungiyar Ansarullah a matsayin wadanda suka kauce ma hanya.
3172257