IQNA

Mutane Uku Sun Samu Raunuka A Wani Hari Kan Cibiyar ‘Yan Shi’a A Najeriya

23:31 - April 21, 2015
Lambar Labari: 3187673
Bangaren kasa da kasa, akalla mutane uku ne aka tabbatar da sun samu raunuka sakamakon wani harin kunar bakin wake da wani dan ta’adda ya kai kan wata cibiyar mabiya mazhabar shi’a a Najeriya.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ina cewa, wasu rahotanni sun ce mutane 3 ne aka tabbatar da sun samu raunuka sakamakon wani harin ta’addanci na kunar bakin wake da wani dan ta’adda ya kai kan wata cibiyar mabiya mazhabar shi’a a garin Potiskun na jahar Yobe da ke arewa maso gabacin Najeriya, yayin da wanda ya kai harin shi ya halaka.
Dan ta’addan ya isa wurin ne da yamma bayan kamala sallar inda mutane kan taru domin tattauna batutuwa da suka shafi lamurransu na addini kamar yadda suka saba yi, amma mutumin ya shammace su inda ya kai kansa da nufin kashe adadi main a mutane a wurin, amma Allah ya taimka ta yadda bam din ya tashi da shi kafin ya kashe mutane.
Babu wata kungiya da ta sanar da alhakin kai wannan hari na ta’addanci, amma tuni mahukunta  abangaren tsaro suka nuna yatsan tuhuma ga kungiyar nan ta Boko Haram, wada ta saba kai irin wadannan hare-hare na ta’addanci a garin, da kuma wannan wuri musamman a lokutan baya.
Tuni dai yan uwa musulmi mabiya tafarkin iyalan gidan manzo na garin suka sanar da cewa an shawo kan lamarin kuma babu wanda ya rasa ransa in banda wanda ya kai harin kunar bakin waken.
3184470

Abubuwan Da Ya Shafa: najeriya
captcha