Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alshuruq cewa, a jiya Ahmad Tayyib babban malamin jcibiyar Azhar ya gana da tawagar malaman Ahlu sunan na kasar Iraki ind a suka jaddada wajabcin yin aiki tare domin samun hadin kan musulmi domin maslahar al'umma.
Jami’ar Al-Azhar ta kasar Masar ta kirkiro wata cibiya ta yanar gizo a kokarin da take yin a fada da tsaurin ra’ayi na addini da ya fara zama karfen kafa ga kasashen duniya musamman kasashen musulmi.
Yayin da yake sanar da hakan, Shuman daya daga cikin manyan jami’an Jami’ar ta Azhar ya ce a halin yanzu dai bisa la’akari da irin yadda masu tsaurin ra’ayin suke amfani da hanyoyin sadaukar na zamani wajen yada akidunsu don haka ya zama wajibi a kirkiro hanyoyi na zamani wajen fada da wannan shiri na su.
Jami’in ya kara da cewa ta hanyar wannan sabuwar cibiyar za a sami damar wayar da kan mutane kan hakikanin koyarwar Musulunci da kuma rashin ingancin abubuwan da masu tsaurin ra’ayin suke yadawa da kuma hanyoyin da suke bi wajen janyo hankulan mutane zuwa gare su.
Cikin ‘yan watannin baya-bayan nan dai Jami’ar ta Azhar ta fito fili da sukar akidu musamman akidar wahabiyanci wanda shi ne tushen irin wannnan tsaurin ra’ayi da ke yawo a duniyar musulmi.
3177923