Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bawwaba News cewa malamin Masar ya bayyana bata sunan musulunci bas u da waalaka da shi.
Babban malamin addinin muslunci mai bayar da fatawa a kasar Masar Sheikh Shauqi Al-allam ya bayyana cewa kungiyar da ake kira Daular Musulunci a Iraki da Sham gungu ne na 'yan ta'adda tantagarya.
A cikin wani bayani da ofishin da ke a cibiyar Darul Ifta a birnin Alkahira ya fitar a jiya Talata, Sheikh Al-allam ya ce 'yan ta'addan kungiyar ISIS bai halasta ba a shar'ance a danganta su da addinin musulunci, domin dukkanin abin da suke yin a ta'addanci da sunan jihadi a cikin kasashen Syria da Iraki ya yi hannun riga da addinin muslunci da kuma koyarwar sunna irin ta manzon Allah.
Shehin malamin ya yi Allawadai da rusa kabrukan annabawa da salihan bayi gami da masallatai da majami'oi da 'yan kungiyar ta ISIS suke yi yanzu ahak a cikin kasashen Syria da Iraki, tare da muzantawa da kuma cin zarafin marassa rinjaye da suka mamaye yankunansu, musamman kiristoci da kuma Izidawa da kuma sauran bangarori na musulmi sunna da.