Kamfanin dillancin labaran iqna ya habrta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na veto cewa, an gudanar da wannan zaman taron karaw ajuna sani a jami'ar tare da halartar malamai daga bangarori daban-daban na kasar.
Abdulfattah Al-awari she shugaban bangaren koyar ilmin fikihu na jami'ar Azahar, shi ne kuma ya jagorancin zaman taron wanda yay i dubi kan muhimman batutuwa da suke da bukatar bahasi a takanin malamai musamman ma malaman kur'ani, danagne da batun nauoin tafsiri da kuma banbancin da ke tsakanin masu ilmin tafsiri.
Bayanin ya ci gaba da cewa wanann taro ya mayar da hankali dangane da wuraren da aa samu banbancin fahimta a kansu tsakanin malamai da kuma yadda zaa kusanto da mahanga da zata dace da abin da ya fi kusa da fahimtar kowa, ta yadda za a rage sabanin da kuma nisan banbancin da ke tasakanin malaman.
Wanann taro dai ya samu halatar malamai daga sassa na kasar ta Masar da ma wasu daga kasashen ketare da suke yin zanari a jami'ar a bangaren addini, musamman a bangaren tafsirin kur'ani mai tsarki, da kuma ilmomin da suke da alaka da shi.
3209083