IQNA

Ma'aikatar Kula Addini ta Palastine Ta Yi Allawadai Da Rufe Kofar Haramin Ibrahimi

0:00 - April 28, 2015
Lambar Labari: 3219775
Babngaren kasa da kasa, Ma'aikatar kula da harkokin addinin muslunci ta Palastine ta yi kakakusar suka dangane da rufe kofar shiga masallaci annbi Ibrahim da yahudawan sahyuniya suka yi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ina cewa, a jiya bangaren kula da harkokin addinin muslunci ta Palastine ta yi kakakusar suka dangane da rufe kofar shiga masallaci annbi Ibrahim da yahudawan sahyuniya suka yi tun bayan kisan gillar da suka yi wani bapalastine.
Ismail Abu Halawa babban daraktan cibiyar ya ci gaba da cewa haramtacciyar kasar Isra'ila ta dauki wannan mataki nesakamakon tabagazar da suka yi a kan al'ummar ankinda kuma tsoron abin da zai biyobaya bayan kisan bapalstinan.
Gwamnatin yahudawan sahyuniya tan adaukar irin wadannan matakai a duk lokacin da ta aikata wata barna, domin kuwa tan ada cikakkiyar masaniya dangane d amartanin palastinawa a kanta, domin kuwa ba su barin jinin shahidansu.
Yanzu haka dai sojojin yahudawan da 'yan sandansu sun dauki kwararn matakan tsaro a dukkanin hanyoyin da lunguna na birnin, domin hana afkuwar duk wata tarzoma ko kuma wani aiki na daukar fansa a knsu.
3210215

Abubuwan Da Ya Shafa: PLS
captcha