Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dillancin labaran kasar Faransa cewa,a jiya kimanin yahudawan Ehiopia mazauna haramtacciyar kasar Isra’ila sun gudanar da wani gangami a birnin Qods domin nuna rashin amincewa da wariyar da ake nuna musu a matsayinsu na bakake fata.
Yahudawan sun yi niyar tafiya ofishin firayi ministan haramtacciyar kasar Isra’ila da ke birnin domin kai kokaensu, amma yan sandan haramtacciyar kasar yahudawan sun hana su, inda suka yi amfani da kulake da barkonon tsohuwa domin tarwatsa su.
Ragotanni sun tabbatar da cewa an kame byu daga cikin masu jerin gwanon, kamar yadda kuma wasu uku daga cikinsu sun samu raunuka, sakamon basu kasha da kulake da kuma har musu hayaki mai sanya hawaye da yan sanda suka yi.
3237950