Kamfanin dillancin labaran iqn aya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sahafaquna cewa, a shekarar bana an ga hukumar alahazan kasar Pakistan ta bayar da fam da a cikinsa a ke tamabayr maniyyaci shi dan shi’a ne ko dan sunna, kuma dole ne ya bayyana mazhabarsa.
Jaridar International Business Times ta bayyana cewa ta ji daga bakin hukumomin alhazai na Pakistan cewa cewa lallai akwai wannan batu, kuma Saudiyya ce ta dage a kan dole saiu an sanya hakan a cikin tambayoyin da za a yi maniyyaci.
Har yanzu dai hukumomin na Saudiyya sun ki su ce uffan kan wanna batu, na tambayar mahajjaci kan cewa shin shi dan shi’a ne? haka nan kuma maukuntan wahabiyawan na Saudiyya bas u bayyana cewa ko za su yi amfani da wannan salon a wasu kasashen musulmi.
Bisa la’akari da irin wadannan take-taken gwamnatin wahabiyawan saudiyya, za a iya cewa aikin hajjin bana zai zama cike da rudani, domin kuwa ga dukkanin alamu akwai shiri na musamman na kawo tarzoma da sunan banbancin mazhaba a tsakanin maniyyata, ko hankoron hana su halartar hajjin baki daya.