IQNA

Malaman Wahabiyawa Baharai Suna Cin Zarafin mabiya Mazhabar Shi’a

23:57 - May 03, 2015
Lambar Labari: 3250572
Bangaren kasa da kasa, an nuna wani faifan bidiyo a cikin shafun yanar gizo na internet inda wasu malaman wahabiyawa ke cin zarafin mabiya mazhabar shi’a a kasar Bahrain.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Mir’atun Bahrain cewa, an samu faifan bidiyo a cikin shafun yanar gizo na internet da ake nunawa, ta yadda wasu malaman wahabiyawa ke cin zarafin mabiya mazhabar shi’a a kasar Bahrain a bayyane ba tare da wani boyo ba.
Wannan matai dai y azo sakamakon irin matakan da ita kanta masautar take dauka ne na hankoron ganin ta mayar da duk mabiyin mazhabar Ahlul bait (AS) a kasar saniyar ware a cikin dukkanin lamurra, wadanda ska shafi siyasa ne ko kuma na zamantakewar yau da kullum na al’ummar kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa wasu daga cikin masu aikata wannan dabbanci ba yan kasar ba ne, an kawo su ne daga kasashen ketare domin gudanar da wannan mummunan aiki tare da lasisin masarautar  wadda ta ke yin biyaya ido rufe ga manufofin wahabiyanci.
Al’ummar kasar Bahrain sun jima suna fuskantar wariya da zalunci daga mahukuntan kasar wadanda suke samun cikakkiyar kariya daga kasashen yammacin turai masu raya dimokradiyya da kuma kare ta a duniya dsaidai da son ransu da kuma maslaharsu ta siyasa, yayin da abin da ke faruwa a Bahrain yake karyata a bin da suke rayawa.

3247162

Abubuwan Da Ya Shafa: bahrain
captcha