Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Nahrain Net cewa, Sheikh Muhammad Nemir y ace idan har gwamnatin Saudiyya ta yi gigin zartar da hukuncin kisa kan Ayatollah Nemir, to kuwa hakan shi ne masomin kawo karshen mulkin Al Saud baki daya.
Mahukuntan na Saudiyya sun yanke hukuncin kisa ne kan Sheikh Al-Nimir Nimir daya daga cikin manyan malaman addinin Musulunci mabiya mazhabar Shi’a a kasar ne bayan kama shi a gidansa, tare da cin zarafin iyakansa da kuma kokarin kashe shi a lokacin kama shi, amma Allah ya hana su cimma burinsu.
Wata kotun da ke shari’ar manyan laifuka a kasar Saudiyya ce ta fitar da hukuncin kisa kan Sheikh Al-Nimir Nimir malamin addinin Musulunci kuma mai rajin kare hakkokin al’ummar da ake zalunta mabiyin mazhabar iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka dan kasar ta Saudiyya kan zargin kunna wutar fitina tare da bijirewa shugaban Musulmi wato sarkin kasar.
Sheikh Al-Nimir Nimir dai ya yi fice a fagen kare hakkokin al’ummar Saudiyya musamman ‘yan tsirarun kasar mabiya mazhabar shi’a tare da nuna kin amincewa da bakar siyasar zaluncin mahukuntan Saudiyya gami da nuna goyon baya ga al’ummun da ake zalunta a duniya musamman al’ummar kasar Bahrain da ke makobtaka da Saudiyya.
Yanzu haka dai wannan batu na shehin malamin yana ci gaba da daukar hankulan al’ummomin dunya, inda ake ci gaba da matsa lamba kan gwamnatin ta Saudiyya da ta gaggauta sakinsa.