Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, Sheikh Ahmad Farhat ya rasu ne a unguwar da yake zaune a ta Nasra cikin birnin Alkahira na kasar ta Masar bayan fama da rashin lafiya da kuma tsufa.
An haife shi ne a garin Amanufiyyah da ke cikin kasar ta Masara cikin shekara ta 1925, kuma ya hardace dukkanin alkur’ani mai tsarki tun yanada da shekaru 12 da haihuwa yana cikin kuruciyarsa.
Sheikh Ahmad Farhat ya shahara ta fuskar karatu da kuma tafsirin kur’ani mai tsarki a kasar, ya kuma karatunsa na addini a cibiyoyi da dam da suke da alaka da cibiyar Ilimi ta Azahar, a cikin shekara ta 1951 ya kammala karatnsa ajami’ar ta Azhara a reshenta da ke birnin Alkahira, daga nan kuma ya zama limamin masallacin Imam Hussain (AS) da ke cikin birnin.
Ya yi rubuce-rubuce da dama a musamman bangaren tafsiri da kuma shari’a bisa tafarkin sunnar manzo, kamar yadda kuma ya mayar da hankali wajen koyarwa da ilmantar da mutane da fadakarwa muhimamn abubwqa da suka shafi musulmi, musamman ma lamurra na addininsu.
Sheikh Farhat ya rayua cikin iyalai masu riko da koyarawr addinin muslunci, da kuma kyawan dabiunsa da suke burge kowa, kuma rasu yana da yaya 6 da ya haifa a rayuwarsa.
3290833