IQNA

Kungiyar Kare Palastinu Ta Fitar Da Bayani Dangane Da Ranar Nakba

23:51 - May 14, 2015
Lambar Labari: 3302851
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kare hakkokin palastinawa ta fitar da bayani da ke cewa Palastinu hakkin mabiya addinin mulsunci ce tare da yin tir da mamamyar yahudawan sahyuniya.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Qudsuna cewa, artabun da aka yi tsakanin dakarun mamaya na Isra'ila da kuma matasa masu gudanar da zanga-zangar zagayowar ranar Nakba wato ranar bakin-cikin a Palasdinu 67 wato 14 na watan Mayu 1948, ya yi sanadiyyar raunata Palasdinawan a yau.

Mafi yawa daga cikin wadanda suka samu raunuka mazauna garin qalandiyya ne wadanda suka yi bata-kashi da daruruwan sojoji da kuma 'Yan sandar HKI da aka tura zuwa yankin domin hana wa jama'a gudanar da zanga-zanga a wannan rana wacce bisa ga al'ada Paladinawa a duk fadin duniya ke amfani da ita domin kara nuna bakin cikinsu dangane da kirkiro kasar da ake kira da suna Isra'aila a ranar 15 ga watan Mayun 1948.

Fiye da palalstiniwa dbu 750 ne suka rasa rayukansu sakamakon wanna mamaya, a can ma yankin Yamma na kogin jodan an gudanar da irin wannan zanga-zanga ta tunawar da ranar bakin ciki, kamar dai yadda aka gudanar da ita a garuruwa.

Sojojin Sahayoniya sun tarwatsa zanga-zangar palasdinawa da su ke juyayin ranar kwace musu kasa da kafa h.k. Isra'ila.Sojojin h.k. Isra'ilan sun yi amfani da karfi domin hana masu zanga-zangar tsallake wani shinge na soja da ke kusa da kauyen Na'alin a yamma da garin Ramallah.

Da safiyar yau talata ne dai sojojin sahayoniya su ka kai farmaki akan palasdinawa ta hanyar amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma harsashin roba.

3300728

Abubuwan Da Ya Shafa: PLS
captcha