IQNA

Ana Shirin Korar Wani Magajin Gari A Farasansa Saboda Kyamar Musulunci

23:48 - May 17, 2015
Lambar Labari: 3304639
Bangaren kasa da kasa, Jam’iyyar Nicola Sarkozy tsohon shugaban kasar Faransa na shirin korar wani magajin gari saboda yin kalaman batunci kan addinin muslunci.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na novelobs cewa, Nicola Sarkozy ya yi Allawadai da kakakusar murya dangane da cin zarafin da mutumin ya yi wanda yake rike da mukami a karkashin inuwar jam’iyyar tasa, inda ya ce ba zai amince da hakan ba a jam’iyyarsa ta UMP.

Shi Ma magajin gari Christian Strozy ya bayyana cewa, yanzu haka sun fara daukar dukkanin matakan da suka dace domin cire magajib garin Rober Shardon wanda ya yi cin zarafi da kamalan batunci kan addinin muslunci, domin hakan ya sabawa dukaknin kaidoji da dokoki na jamiyarrsa.

Wannan mataki dai yana daga cikina bubuwan da ake ganin zai baiwqa jam’iyyar farin jinni a tsakanin mabiya addinin muslunci yan kasar Faransa a zabuka masu zuwa, musamman a yankunan da suka fi yawa, sakamakon wannan mataki na ba sani babu sabo da jam’iyyar ta dauka kan magain garin.

Nocola Sarkozy ya bayyana cewa yan atare da musulmi tsawon shekaru hatta acikin jam’iyyarsa, kuma wannan jamiya ba a gina kan gaba da kiyayya da wani addini ko wata al’umma ba, saboda haka za su bari wani ya shigo musu da wata mummunar hanya ba a cikin tafarkinsu.

3304488

Abubuwan Da Ya Shafa: faransa
captcha