Mukhtar Muhammad Mahmud mahardacin kur’ani mai tsarki da ya halarci gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki da tundiya,a zantawarsa da kamfanin dillancin labaran iqna ya ya bayyana cewa yin aiki da koyarwar kur’ani mai tsarki ne kawai hanyar yin yaki da tsatsauran ra’ayi da ke barazana ga wanbann al’umma.
Ya ci gaba da cewa wajibi ne da ya rataya kan al’ummar musulmi baki daya aduk inda suke su hada kai, su yi watsi da dukwani batun banbancin mazhaba ko abin da ya yi kama da haka, domin ain da ya hada musulmi ya fi wanda ya raba su.
Su yi aiki da fadar Allah madaukakin sarki da ke cewa “Ku riko da igiyar Allah kada k rarraba” domin hakan ne kawau hanyar mayar da martini ga masu giramn kai na duniya da babban burinsu shi ne haifar da fitina da rarraba tsakanin al’ummar musulmi.
Wanann mahardacin kkur’ani mai tsari ya kara da cewa, dangane da rayuwarsa ya hardace kur’ani ne tun yan adan shekaru 14 da haihuwa, kuma ya yi hakan ne a kasarsa tun yana karami tare da taimakon mahaifansa da ska dora shi kan tafarkin karatun kur’ani mai tsarki da kuma hanyar hardarsa.
Y ace halarci gasar karatu da harda a kasashen duniya daban-daban kuma ya samu nasarori masu yawa a wannan fage na harda musamman, kuma yana fatan a gasar kur’ani da ake gudanarwa yanzu haka da yake halartar a jamhuriyar musul;unci ya samu nasara.
3304864