Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al-alam cewa, Tzipi Hotovely sabuwar mataimakiyar ministan harkokin Haramtacciyar Kasar Isra'ila ta bayyana cewa, tun daga gabar yamma ta kogin Jordan abin da ya hada dukkanin Palastinu har zuwa gabar ruwan tekun Mediterranean duka mallakin yahudawa ne.
Tzipi Hotovely dai yar jam’iyar Lekud ce ta firayi ministan haramtacciyar kasar yahudawan Benjamin Netanyahu, wadda ta shahara wajen kiayya da al’ummar palastinu da kuma larabawa tun bayana da ta bayyana a fagen siyasa a tsakanin yahudawa.
Tun kafin wannan lokacin dai ta kasance a sahun gaba wajen kin amincewa da duk wani batu na kafa kasar palastinu ma cin gishin kanta, kamar yadda kasashen duniya suka nema, domin samun zaman lafiya mai dorewa a tsakanin yahdawa da kuma palastinawa, wanda kuma hakan na daga cikin salon siyasar jam’iyyar tasu.
Tzipi Hotovely tana nakalto wata Magana ce daga wani daya daga cikin fitattn malaman yahudawa akasar faransa da ke cewa, wannan kasa mallakin yahudawa ce baki daya, bab wani mahaluki da yake da hakki a cikinta, yana nufin wurin da suka fa haramtacciyarsu.
3306695