Kmafanin dillancin labaran iqn aya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-wasat cewa, wannan shi ne karo na hudu da akae gudanar da wannan gasa wadda ta kebanci mata kawai kuma ana gudanar da harda ne da kuma karatu gami da tajwidi a garin na Sabha da ke arewacin kasar.
Rukayyah Al-barshi ita ce dai tsohuwa yar shekaru 98 wato mafi yawan shekaru a tsakanin dukkanin matan da suke halartar wannan gasawadda ita ma ta shiga gasar hardar kur’ani mai tsarki a garin Sabha domin kara karfafa gwiwar mata makaranta da mahardata kan lamarin kur’ni mai tsarki.
Salima Abdulsalam daya daga cikin masu sanya ido kan yadda ake gudanar da wannan gasa ta bayyana cewa, an kasa gasar ne har kasha biyu, kasha na farko ya kunshi mata magidanta zalla, sai kuma kasha na biyu ya kunshi yan mata masu kananan shekaru da kai ga yin aure ba, sai kuma yara maza kanan da suke harda ko karatun kur’ani mai tsarki.
Ta kara da cewa yanzu haka dai akwai masu halartar gasa da kumamahardata da makaranta 60, amma mafi girman shekaru daga cikins ita Ruqayyah Muhammad Al-barshi wadda ke da shekaru 98, wadda kuma har yanzu ana ci gaba da karawa da ita a fagen harda.
3307915