Kamfanin dillancin labaran Iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gioz na ISESCO cewa, za a gudanar da taron ne a ranar Juma’a mai zuwa abirnin na Kotono tare da halartar shugaan kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa an zabi birnin Kotono na kasar Benin a matsayin babban birnin al’adun muslunci a nahaiyar Afirka ne na wannan shekara da nufin kara dankon zumuntaka tsakanin dukanin kasashen musulmi na nahiyar a mataki na Afirka.
An gudanar da wai biki makamancin wannan a birnin Nazwi na kasar Oman, inda aka zabi birnin a matsayin bababn birnin al’adun muslunci a cikin kasashen larabawa, haka nan kuma an zabi birnin Almati Qazagestan a matsayin babban birnin al’adun usluncia cikin nahiyar Asia na shekara ta 2015.
Daga cikin wadanda za su halarci taron kuwa har wakilai na kungiyoyin kasa da kasa, da suka hada da na kungiyar raya ala’dun kasashen musulmi, da kuma na kungiyar hada kan kasashen muslmi, gami da wasu daga cikin daga cikin cibiyoyin raya al’adu na nahiyar.
Manufar irin wadannan taruka dai it ace kara kusanto da fahimtar al’aumomi muslmi, tare da kara karfafa dankon fahimtar juna da zaman lafiya tsakaninsu da dukkanin al’ummomin duniya, ba tare da samun rashin jituwa ba.
3308451