Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo jaridar youm Sabe cewa, yanzu haka , jami’ar Azhar ta kasar Masar na shirin aiwatar da wani shiri shiri na musamman na kur’ani mai tsarki wada shi ne na farko a irinsa a tarihinta.
Jami’ar Azhar dai tana gudanar da shirye-shirye na addinin musluncia cikin wannan lokaci da nufi kafa bunnksa ayyuka da suka shafi kur’ani mai tsarki daga nan har zuwa cikin watan azumi, shirin na wanann lokaci zai shafi ‘yan kasa da shekaru 40 ne da haihuwa.
Kuma a kowane lokaci tana yin kokari domin kara inganta irin wadannan shirye-shirye, rijistar sunayen wadanda suke bukatar shirin dai zai fara ne daga ranar 13 zuwa 30 ga watan sha’aban mai alfarma.
A cikin watan azumi ne dai shirin zai kankama yadda ya kamata, za a bayar da dama ga dukaknin mahalarta shirin da su kasance cikin shiri domin gudanar da gasar a dukkanin bangarori da ska shafi karatun kur’ani mai tsarki.
Babban abin da ake bukata dais hi ne sanin kaidojojin karatu, da kuma kyawun sauti, wanda shi ne za a tantace dukkanin matakai a cikin gasar, kama daga na daya na biyu har zuwa na ku a dukkanin bangarorin da aka bayyana.
Za a watsa shirin kai a kafofin sadarwa na talabijin da kuma yanar gizo da za a iya gani, da kuma tashoshin tauraron dan adam.
3308651