IQNA

Sahyuniya Sun Hana Kiristoci Gudanar Da Tarukansu Na Addini

23:55 - June 03, 2015
Lambar Labari: 3310849
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin yahudawa masu tsatsauran ra’ayi sun hana wasu kiristoci gudanar da tarukansu an addini a Jabal Sahyun da ke yammacin birnin Qods.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Palastinawa cewa, gomomin yahudawan masu tsatsauran ra’ayi sun hana wasu kiristoci gudanar da tarukansu an addini a Jabal Sahyun da ke yammacin birnin mai alfarma.

 

Bayanin ya ci gab ada cewa a kowace shekara mabiya addinin kirista kan halarci wannan wuri saboda matsayinsa a tarihin annabawa da ke komawa tun lokacin annabawa, jami’an tsaron tsaron haramtacciyar kasar yahudawan sun yi amfani da karfi domin tarwatsa masu tsatsauran ra’ayin.

Tarihin wurin dai yana da alaka ne da annabi Dawud (AS) inda a nan makabrtarsa take, tun bayan kafa haramtacciyar kasar Isra’ila a cikin shekara ta 1948, sun mayar da wurin daya daga cikin muhimman wurarensu, tare da daukar matakai na hana sauran mutane ziyara, duk kuwa da cewa dukaknin mabiya addinai da aka safkar daga sama suna da hakkin ziyartar wurin.

 

Tun bayan da yahudawan sahyuniya suka kwace iko da wannan makabarta ta annabi Dawud (AS) sun mayar da kiristoci kawai masu zuwa yawun shakatawa a wurin, amma ba dai masu alaka ta addini da wurin ba.

3310639

Abubuwan Da Ya Shafa: Qods
captcha