Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarawa na yanar gizo na mabiya tafarkin iyalan gidan manzo a Pakistan cewa, al’ummar Kuita na kasar Pakistan sun gudanar da tarukan tsakiyar watan Sha’aban domin gudanar da bukukuwan tuawa da zagayowar lokacin haihuwar Imam Mahdi (AJ) kamar dai yuadda suka saba yi.
Mutanen yanki dai sun jima sun fuskantar matsaloli musamman a cikin yan shekarun nan daga yan ta’adda masu kai hare-hare a kansu saboda banbanci na fahimta, wanda kuma hakan ya zama babbar matsala wadda take kara raba kan al’umma.
Duk da haka mutanen suna yin iyakacin kokarinsu domin ganin sun zauna da sauran mutane mabiya wasu mazhabobin na daban lami lafiya ba tare da wani tashin hankali ba, duk kuwa da irin tsokanar da yan ta’adda suke yi musu, wadanda suke samun goyon baya daga wasu mutanen yankin.
Tarukan tunawa da haihuwar Imam Mahdi (AJ) na daga cikin ayyukan da mabiya tafarkin iyalan gidan manzo na kasar suke gudanarwa a kowace shekara a tsawon tarihinsu na daruruwan shekaru da suka gabata.
3310336