IQNA

An Fara Gudanar Da Gasar Kur’ani Mai Tsarki Ta Kasar Malayzia

23:52 - June 10, 2015
Lambar Labari: 3313153
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar karatu da hardar kur;ani mai tsarki ta duniya daga kafe 9 zuwa karfe 13 a cikin babban ginin cibiyar kasuwancin kasar.


Dan rahoton kamfanin dilalncin labaran Iqna daga Kualalampour ya habarta cewa, daidai da yadda aka tsara da karfe 9 daidai ne na safe aka fara gudanar da wanann gasa tare da halartar bakin da suka zo, da kuma alkalai daga kasahe daban-daban da zasu sanya ido kan gasara  dukanin bangarori, duk kuwa da cewa daga bisa da aka shiga bangarorin gasar adadin wadanda ke wurin ragu.

Bayanin ay ce bangaren farko ya fara daga 9 zuwa 10:30, bayan nan an yi hutun mintuna 15, daga nan kuma an koma a karfe 10:45 har zuwa kafe 12:00 na rana daidai, bayan nan kuma na tashikowa ya koma masafkinsa domin hutawa, inda aka koma karfe 20:00 na yammaci ha zuwa dare.

Wadanda suke halartar gasar dai sun fito ne daga kasashe fiye da 70 da suka hada da na musulmi da kuma wadanda ban a musulmi kamar yadda aka saba, kuma gasar za ta daui kwanaki 5 a jere ana gudanar da ita.

3312921

Abubuwan Da Ya Shafa: Malayzia
captcha