Kamfanin dilalncin labaran Iqn aya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar Enghlab cewa, karamin ofishin jakadancin Irana kasar India ya tabbatar da cewa wadannan mutane sun yi cincirindo a gaban masalalcin daga bisani kuma suka afka masa suka kwace iko da shi.
Dangane da haka Maulana Sayyid Mahmud Madani daya daga cikin malamai a yankin ya kafa kwamiti domin bin kadun lamarin ta hanayar lumana, tare da warware matsalar ba tare da an kai ruwa rana.
Mabiya addinin muslunci a kasar ta India suna fuskantar barazana daga kungiyoyin Indiawa masu tsauran ra;ayi da ke kai musu farmaki tare da kwace musu dokiyiyi da kaddarori lokaci zuwa lokaci, wanda hakan yake nuni da matsalar da musulmin yankin suke ciki.
Maulana Madani y ace wannan masallacin mallakin musulmi ne kuma za su yi amfani da hankali domin domin dawo da hakkinsu.
3312823