Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bernama cewa, Ahmad Aiman Dabbus daga garin Tripoli na Lebanon na daga cikin makaranta 11 da suka yi karatua dare na biyu na gasar.
Ya bayyana hakartarsa a wannan gasa da cewa tana daga cikin abubuwa masu matukar muhimmanci a cikin tarihin rayuwarsa, musamman ma ganin cewa shi ne mafi karantar shekaru kuma ya samu wannan babbar dama.
A cikin bayanin nasa ya ce su 5 a gidansu, amma tun yan adan shekaru 7 da haihuwa mahaifansa suka taimaka masa wajen karatu da kuma hardar kur’ani mai tsarki, kuma ya samu nasarar akiwa ga manufarsa, bayan da aka saka shi marantar harda.
Mahifinsa shi ne Fu’ad Dabbus da shekaru 44 da haihuwa, mahaifiyarsa kuma ita ce Luba Danawi, sun bayyana matukar gansuwarsu dangane da kokarin da yaron nasu yake wajen gudanar da karatunsa kamar yadda yake yi a halin yanzu cikin nasara.
3313657