Kamfanin dilalncin labaran Iqna daga birnin Kualalampour na kasar Malaysia ya habarta cewa, a gasar kur'ani mai tsarki ta duniya da aka gudanar a kasar makaranci kuma maharadacin kur'ani mai tsarki Muhsin Hajj Al-hasani daga kasar Iran, ya lashe gasar a bangaren tilawa, amma kuma ba a kira shi a bangaren tilawar rufe gasar ba kamar yadda aka saba yi.
Bayanin ay ci gaba da cewa koshakka abin da ya faru ya sabawa abin da aka saba iawatar a duk lkacin da aka gudanar da wata gasar kur’ani ta duniya awata kasa, inda akan kira mutum da yay a zo a na daya a bangaren tilawa domin yin karatun fufe taron gasar.
Mohsen Haji Hasani Kargar ya bayyana abin da ya faru da cewa ba komai ba ne a wurinsa duk da cewa dai ba a yi kamar yadda aka sab aba, abu mafi muhimmanci shi ne samun damar halartar gasar da Allah y aba shi, kuma har ya samu nasarar lashe gasar baki daya.
Ya ce yana mai fatan gudanar da irin wadannan taruka su zama sanadiyyar kara bunkasa ayyuka da suka danganci kur’ani mai tsarki a cikin kasashen musulmi da ma duniya baki daya.