IQNA

Manhajar Muslim Face Za Ta Fara Aiki A Cikin Watan Ramadan

17:56 - June 15, 2015
Lambar Labari: 3314814
Bangaren kasa da kasa, manhajar nan ta yanar gizo da ake yin amfani da wayar salula domin kamata ta Muslim Face mai mambobi 1000 za ta fara aiki ne a cikin wannan wata na Ramadan mai zuwa.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gioz na Ina cewa, Shu’aib Fida’i da kuma Ruhul Amin Shu’ab su ne suka samar da wannan hanya ta Muslim Face tun watannin da suka gabata, amma sun sanya za ta fara  aiki a cikin wannan wata mai afarma.

Wannan hanyar dai ta fara ne da mambobinta 1000 kuma daga bisani ta ci gaba da karbar masu bukatar shiga domin karuwa, musamman ma ganin cewa abubuwanda ake sakawa a ciki kowa zai iya amfana da sua  cikin dukkalnin lamurra.

A ciki akwai harsunan turancin English, Larabci, Farsi, Urdu, Malayu, Turkanci da kuma yaren Indonesia, kamar yadda kuma ake da shirin kara wasu daga cikin harsuna a nan gaba domin amfani musulmi a duk inda suke da kuma harshen da suke yin Magana da shi.

Da dama daga cikin wadanda sua fara amfana da shirin da sun nuna gamsuwarsu matuka, kuma sun nuna cewaa  shirye suke su bayar da dukkanin gudunmawa domin ci gaban lamarin na MuslimFace da ke da alaka da kamfanin Muslim Face Limited, kamar dai yadda aka yi wa shafin rijista.

3314462

Abubuwan Da Ya Shafa: Face Muslim
captcha