Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Mir’ar Bahran cewa, masarautar mulkin mulukiyya ta kasar Bahrain ta yanke hukuncin daurin shekaru 4 a gidan kaso kan Sheikh Ali Salman, babban sakataren Jam'iyyar Al-wifaq, jam'iyyar siyasa mafi girma a kasar, saboda matsayarsa da ke neman a yi adalci a cikin harkokin mulki, maimakon bin salon mulkin kama karya a kasar ta Bahrain.
Abdulalh Alshmlawi daya daga cikin lauyoyi masu kare sheikh Ali salman ya bayyana cewa, wannan hukunci ba shi da wata kima ta fuskar shari’a, domin kuwa hukunci ne da aka gina kan manufa ta siyasa.
Sheikh Ali Salman dan shekaru 50 da haihuwa ya kasance daya daga cikin fitattun masu gwagwarmaya domin fadakar da jama’a dangane da hakkokinsu da aka danne musu a kasar Bahrain, kuma an kame shi ne bisa wadannan dalilai na siyasa.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa ta fitar yana dauke da sanarwar cewa; Mahukuntan gidan sarautar Bahrain suna tsare da Sheikh Ali Salman babban sakataren jam’iyyar Al-Wefaq kuma jagoran ‘yan adawar kasar ne saboda furta albarkacin bakinsa ta hanyar lumana, don haka tana kira ga mahukuntan Bahrain da su hanzarta sakinsa ba tare da gindaya wani sharadi ba.
3315171