Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jarodar Youm Sabe cewa, kasashen Saudiyyah, UAE, Qatar, Kuwait, Masar, Yemen, Jordan da Bahrain sun ce ranar laraba ce ranar karshen watan shaban, kuma gobe ne farkon azumi. Su ma kasashen Malaysia, Indonesia, da Turkiya sun sanar da ranmar gobe Alahamis a matsayin ranar farko ta watan Ramadan mai alfarma. Kasar saudiyya ta bayyana cewa bisa ga lissafin da ta yi a ya ne ake duba watana matsayin duba ta biyu kuma ta karshe, domin kuwa lissafinta ya cika daidai, kuma gobe ne farkon ranar watan Ramadan na wannan shekara. Masu bayar da fatawa na birnon Qods da Syria da kuma Lebanon duk sun bayyana cewa ra’ayninsu shi ne gobe za a dauki azumin watan Ramadan mai alfarma, kamar yadad wasu daga cikin kasashen musulmi suka sanar da hakan daga bangarensu. Daya daga cikin ‘yan kwamitin ganin wata na ofishin Jagoran juyin juya halin Musulunci ya sanar da cewa daga dukkan alamu ranar Alhamis ce za ta zamanto daya ga watan Ramalana na wannan shekarar, amma idan ba a ga wata ba, to Juma’a ce za ta zama daya ga watan. Dan kwamitin ganin watan na ofishin Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa idan kuwa ba a ga watan ba, to za a cika watan Sha’aban don haka Juma’a za ta zamanto daya ga watan Ramalana. Kafin hakan dai masana a ofishin Jagoran juyin juya halin Musuluncin sun sanar da cewa kafin ranar Laraban dai ba zai yiyu a ga wata din ba a ko ina a duniya don haka daga ranar Laraba ce za a fara duban watan na Ramalana.