Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga bangaren labaran yanar gizo na palastinu cewa, a yau yahudawa haramtacciyar kasar Isra’ila sn tsaurara matakan tsaro kan musulmi masu sallar Juma’a a Qods a juma’ar farko ta watan Ramadan da a ke gudanarwa.
Rahoton ya ce tun jiya ne yan sanda yahudawan suka fara daukar irin wadannan matakai domin ganin cewa sun saka shakamaki tsakanin musulmi da kuma wannan masallaci mai albarka, domin kwa sun san cewa musulmi za su halarci ju’ar farko ta watan.
Kafin lokacin sun sanar cewa ba za su bar palastinawa yan shelaru kasa da 40 su gudanar da sallar juma’a ba.