IQNA

Malaysia Ta Bukaci Kasashen Musulmi Su Hada Karfi Da Karfe Domin A Yaki Daesh

20:40 - June 22, 2015
Lambar Labari: 3317485
Bangaren kasa da kasa, Anifah Aman ministan harkokin wajen kasar Malaysia ya yi da cewa kasashen musulmi su hadu domin kawo karshen kungiyar ta’addancin Daesh.


Kamfanin dillancin labaran iqn aya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na IINA cewa, Anifah Aman ministan harkokin wajen kasar Malaysia ya bayyana kungiyar yan ta’adda ta ISIS da cewa abin da take ya sabawa muslunci, saboda hakan ya yi kira da cewa kasashen musulmi su hadu domin kawo karshen wannan kungiyar ta’addanci baki daya.

Ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake halartar taron kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya, inda a gefen taron ya yi wannan kira, tare da tabbatar da cewa ta hanyar hada karfi da kaefe ne kawai za a dawo da martabar muslunci da yan ta’adda suka bata.

Dangane da hare-haren da yan Daesh suke kaiwa kan fararen hula da kuma kisan gillar da suke yi kan mutane a yankunan da suka kwace iko da su, ya ce wannan babban abin takaici ne ga musulmi baki daya.

3317108

Abubuwan Da Ya Shafa: malaysia
captcha