IQNA

Sanarwar hadin gwiwa da kasashen Larabawa da na Islama 31 suka yi kan shirin "Isra'ila Babba"

15:23 - August 16, 2025
Lambar Labari: 3493719
IQNA - Kasashe 31 na Larabawa da na Musulunci da kungiyar hadin kan kasashen kasashen musulmi da kuma kungiyar hadin kan yankin tekun Fasha sun fitar da sanarwar hadin gwiwa inda suka yi Allah wadai da kalaman Benjamin Netanyahu, firaministan gwamnatin Sahayoniya, dangane da shirin da ake kira "Isra'ila Babba".

Al-Mayadeen ya nakalto daga bayanin yana cewa: Kalaman Benjamin Netanyahu dangane da shirin da ake kira "Isra'ila Babba" a fili yake karara ce ga dokokin kasa da kasa, kuma barazana ce a fili ga tsaron kasa na Larabawa, da ikon mallakar kasashe, da tsaro da zaman lafiya na shiyya-shiyya da na kasa da kasa.

Sanarwar ta kara da cewa: Kalaman firaministan gwamnatin yahudawan sahyuniya barazana ce kai tsaye ga tsaron kasa na kasashen Larabawa, da ikon mallakar kasa, da tsaro da zaman lafiya na shiyya-shiyya da na kasa da kasa, kuma kasashen Larabawa da na Musulunci za su dauki dukkan matakan da suka dace don tabbatar da zaman lafiya, tare da kawar da tunanin mamayar da karfin tuwo.

Kasashen Larabawa da na Musulunci sun jaddada a cikin wannan bayani cewa: Muna Allah wadai da kalaman ministan kudin haramtacciyar kasar Isra'ila Bezalel Smotrich dangane da shirin samar da zaman lafiya da kuma kalaman wariyar launin fata da masu tsaurin ra'ayi na adawa da kafa kasar Falasdinu. Muna sake nanata cikakkiyar adawarmu ga yunkurin tilasta wa al'ummar Palasdinu kauracewa gidajensu ta kowace hanya da kowane irin dalili.

Firayim Ministan Isra'ila kwanan nan ya yi iƙirarin a cikin wata hira da cibiyar sadarwar i24: Ina kan manufa ta tarihi da ta ruhaniya kuma ina sha'awar mafarkin Isra'ila Babba!

 

 

4300058

 

 

captcha