Bayan rahotannin da ke cewa wasu cibiyoyin siyasa da na hidima sun yi amfani da hotunan Ayatollah Sayyid Ali Sistani, babban jami’in ‘yan Shi’a na kasar Iraki, a kan tutoci da fastoci da aka sanya a duk fadin birnin, musamman a kan hanyar da mahajjata ke tafiya zuwa haramin Imam Husaini (AS), ofishinsa ya fitar da wata sanarwa da ke nuna rashin jin dadinsa da wannan mataki.
Bayanin ya ci gaba da cewa: An lura da cewa wasu cibiyoyin siyasa da na hidima suna rike da hotunan Ayatullah a wuraren taruwar jama'a a kan tutoci musamman a lokacin tattakin Arba'in na Imam Husaini (AS).
Sanarwar ta kara da cewa: "Muna sake jaddada adawarmu da wannan mataki, muna kuma kira ga kowa da kowa da ya guje wa irin wannan abu, sannan kuma ga bangarorin da abin ya shafa da su dauki matakin da ya dace a kan hakan."