Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Almirsad cewa, a jiya jami’an tsaron kasar Saudiyya a cikin kayan sarki sun keta alfarmar kur’ani mai tsarkia lokacin da suka rusa wani masallaci bisa hujjar cewa an gina shi ba bisa kaida ba a garin Makka mai alfarma.
Al’ummar unguwar Mu’aisam sun bayyana cewa mahukuntan an Saudiyya sun rusa masallacin ne bayan da suka yi Magana cewa ya saba wa kaida, amma an jiye Magana da su sai bayan watan azumi za a sake yin Magana kan yadda za a yi da shi.
Mahukuntan sundauki wannan mataki ne duk kuwa da cewa mutanen wannan unguwa suna gudanar da sallar tarawihi a cikin masallacin a cikin wannan wata mai alfarma, babban abin munin shi ne yadda suka rusa masallacin ba tareda kwashe kayan da ke cikinsa ba da suka hada da alkur’ani mai tsarki.
Abu Hazim daya daga cikin muatnen da ke kula da masallacin y ace za su bi kadun lamarin, domin kuwa su ne da kansu suka gina masallacin ba tare da wani taimako na hukuma ba, saboda gahaka ba za su bari abin ya tafi hakan nan ba.
3318561