Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ina cewa, duk da irin matakan da gwamnatin yahudawa ta dauka palastinawa kimanin dubu 350 ne suka gudanar da sallar Juma’a ta biyu a cikin watan Ramadan mai alafarma a masallacin Aqsa.
Sheikh Azzam Alkhatib babban darakta mai kula da harkokin addinin ba birnin Qods ya bayyana cewa adadin mutane dubu 350 da suka halarci sallar Juma’a a wamnnan mako sun fito daga yankunan gabar yamma d akogin Jordan.
Haka nan Sheikh islamail Nawahidah limamin masallacin Qods ya bayyana cewa albarkacin azumin ewatan Ramadan da kuma neman falalar da ke cikinsa ta sanya mutane yunkurawa domin samun salla a wannan masallaci mai alfarma.
Kafin nan dai jami’an tsaron na Police na haramtacciyar kasar Isra’ila sun hana daruruwan palastinawa daga yankuna daban-daban zuwa sallar Juma’a ta biyu a cikin watan Ramadan mai alfarma a masallacin Qods.
Tashoshin talabijin sun bayar da rahoton cewa adadin palastinawa da aka hana zuwa sallar sun kai kimanin dari biyar daga yankin zirin da aka killace, yayin da kuma sauran wadanda suke yankunan gabacin birnin Qods da gabar yamma ta kogin jodan suka kafa musu sharuddan cewa sai wadanda shekarunsu suka haura hamsin ne kawai za a bari su shiga masallacin mai alfarma domin yin sallar Juma’a a yau.
Gwamnatin yahudawan ta bayyana dalilin hakan da cewa yana da alaka ne da batun tsaro kai tsaye, musamamn ma bayan harba wani makamin roka daga yankin zuwa cikin arewacin palastibnu da Isra’ila ta mamaye a cikin makonni biyu da suka gabata.
3319942