IQNA

Tawagar Da Jagora Ya Tura Kuwait Ta Isa Isa Da Sakon Ta’aziyyah

23:54 - June 29, 2015
Lambar Labari: 3321185
Bangaren kasa da kasa, Ayatollah Tashkhiri a matsayin manzo na musamman daga jagoran juyin juya hali tare da tawagarsa ya isa kasar Kuwait domin isar da sakon ta’aziyar wadanda suka shahada a harin masallacin Imam Sadiq (AS)

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga bangaren hulda da jama’a na cibiyar kusanto da mazhabobin muslunci ta duniya cewa Ayatollah Tashkhiri shi ne dan aike na musamman daga jagoran juyin juya hali tare da tawagarsa ya isa kasar Kuwait domin isar da sakon ta’aziyar wadanda suka shahada a harin masallacin Imam Sadiq (AS) a ranar Juma a da ta gabata.
Ayatollah Muhammad Ali Taskhiri yana tare da manyan mutane da suka hada har da Ayatollah Abbas ka’abi mamba majalisar kwararru masu zaben jagora da ma wasu daga cikin malamai da jami’ai, sn isa kasar ta Kuwait domin isar da sakon jagora ga sarki kasar, da kuma iyalan wadanda ska shahada a masallacin Imam Sadiq (AS) sakamakon harin da aka kai kansu.
A nasa bangaren dan majalisar dokokin kasar Kuwait dashti ya bayyana hare-haren da aka kai kasar a ranar Juma’a da ta gabata da cewa, sakamako ne bin sahun kasashen da ke mara baya ga ta’addanci da kasar Kuwait ke yi.

 

A lokacin da yake zantawa da wasu kafoin yada labarai jiya a kasar ta Kuwait, ya bayyana cewa, babban kuren da aka yi shi ne, yadda Kuwait ta yi zaton cewa mara baya ga kasashen da suke daukar nauyin ta’addanci a kasashen ketare musamman ma na larabawa da ke makwabataka da su maslaha ce ta siyasa a gare ta, ga kuma abin da hakan ya jawo mata, ‘yan ta’addan da suke goyon baya a yau su ne a cikin gida.

Wannan dai shi ne karon farko da ‘yan ta’addan IS suka kaddamar da hare-hare a cikin kasar Kuwait, inda wani dan ta’adda mamba  a kungiyar ta IS dag a kasar Saudiyyah ya tarwatsa kansa da jigidar bama-bamai a tsakiyar masallata a lokacin sallar Juma’a a masallacin mabiya Mazhabar shi’a, inda ya kashe kansa kuma ya yi sanadiyyar rasuwar wasu mutane ashirin da bakwai tare da jikattar wasu fiye da dari biyu.

 

3320849

Abubuwan Da Ya Shafa: kKuwait
captcha