IQNA

Ana Gudanar Da Gasar Kur’ani Ta watan Ramadan A kasar Libya

23:45 - June 30, 2015
Lambar Labari: 3321653
Bangaren kasa da kasa, ana gudanar da wata gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki a garin Zaltain na kasar Libya tare da halartar wasu fitatun makaranta na kasar.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na akhbarlibya.24.net cewa, yanzu haka ana cikin gudanar da wata gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki masallacin Abu Munhal da ke a garin Zaltain na kasar Libya tare da halartar wasu fitatun makaranta na kasar daga sassa daban-daban.

Fu’ad Al-ghawaji masanin kan harkokin kur’ani ya ce wannan gasa tana matukar muhimamnci, domin kuwa sau daya a ke gudanar da irin a kowace shekara watoa  acikin watan Ramadan mai alfarma, inda akan gayyaci makaranta da maharata na kasar domin su halarta.

Alkalan gasar dai dukakninsu yan kasa ne, kuma suna yin iyakacin kokarinsu domin tantance masu karatun a dukkanin bangarori, kama daga bangaren sama da kuma na tsakiya gami da bangare na karshe wanda akasarin masu karatu a bangaren yara ne.

Ya kara da cewa wannan babban abin koyi ne daga al’ummar Libya, idan aka yi lakari da halin da kasar ta k eciki, amma duk da haka mutane suna yin iyakacin kokarinsua  cikin wannan wata mai alfarma domin kula da lamurran kur;ani mai tsarki.

Daga karshe za a bayar da kyutuka ga wadanda suka nuna kwazoa  dukkanin bangarorin gasar kama daga batun harda har zuwa kira’a, wanda hakan ke kara zaburar da matasa ga kurani mai tsarki.

3321543

Abubuwan Da Ya Shafa: libya
captcha