Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gioz na talashr talabijin ta Al-alam cewa, a jiya yan ta’addan Boko Haram sun kashe musulmi kimanin dari da arbain da biyar masu azumi a yakin arewa maso gabacin tarayyar Najeriya, a ci gaba da harin da suke kaiwa.
Kimanin Mutane dari da arbain da biyar ne mayakan boko haram suka hallaka a jihar Borno dake arewa masu gabashin Najeriya. Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa wasu ‘yan bindiga da ake kautata zaton ‘yan boko haram ne sun kai munanaen hare-haren a wasu kauyuka dake jihar borno na arewa maso gabashin Nijeriya a ranar Alkhamis da ta gabata, inda suka hallaka Mutane daga cikinsu a kwai Mata da kananen yara.
Rahoton ya ce fiye da mayakan boko haram 50 ne suka yiwa kauyen kukawa dirar mikiya inda suka tarar da Mutane na salla, bayan sun jira an kamala sallar sun ware Maza da Mata sannan suka kashe kimanin Mazaje 97
A wasu kauyuka biyu mayakan na boko haram sun cinnawa gidajen Mutane wuce tare da hallaka mutane kimanin 50 daga cikinsu harda Mata da kananen yara.
Wannan hari shine mafi muni da kungiyar Boko haram da ta kadamar a Najeriyar tun bayan da aka rantsar da shugaba Muhamad Buhari a matsayin shugaban kasa.