Kamfanin dillancin labaran iqn aya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Deccan Herald cewa, mutane 44 ne suka rasa rayukansu wasu kuma suka jikkata a daren jiya Lahadi sakamakon tashin wasu tagwayen bama-bami a birnin Jos na jahar Palteau Najeriya.
Abdulsalam Muhammad jami’I a hukumar bayar da gajin farko a kasar ya ce bam na farko ya tashi ne a wani gidan cin abinci da ke titin Bauchi a garin na Jos, inda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane ashirin da uku tare da jikkata wasu 67.
Kafin daga bisani kuma wani bam din ya tashi a masallacin ‘yan taya, bayan yin wasu harbe-habe da bindiga a lokacin da shugaban majalisar malamai na kungiyar izala yake gabatar da tafsirin kur’ani mai tsarki, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 18 a nan take, amma rahotanni sun ce daga bisani adadin ya karu zuwa ashirin da daya.
A nata bangaren hukumar bayar da gajin gaggawa ta Najeriya a hukumance ta ce ta ce akalla mutane 67 ne suka samu raunuka sakamakon hare-haren, kuma ana kula da su a asibiti, duk kuwa da cewa wasu daga cikinsu na cikin mawuyacin hali.
Wannan hari dai yana ci gaba da fuskantar kakakusar suka da Allawadai daga sassa daban-daban na Najeriya da ma wasu daga cikin kasashen duniya, tare da bayyana hakana matsayin wani na ta’addanci da kuma dabbanci.
3324122