IQNA

An Sanar da Sunayen Mutane 10 Da Suka Fi Nuna Kwazo A Gasar Dubai

20:39 - July 09, 2015
Lambar Labari: 3326042
Bangaren kasa da kasa, an saar da sunayen mutae 10 wadanda suka fi nuna kwazoa gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta Dubai.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Emarate cewa,a daren jiya ne aka gudanar da bikin girmama wadanda suka halartarci gasar kur’ani ta Dubai da suka hada da wadanda suka fi nuna kwazo.

Bisa sakamakon da aka fitar Faisal Muhammad Alharisi daga Saudiyya, Hamza Alhabashi daga Amurka, Muhamad zakariyya daga Bangaladash, Abdlrahim Siyamsuri daga Indonesia, Muhammad Mahmud daga Libya, Abdulmajid daga Yemen, Alfatih daga Sudan, Sinjar Khaid daga Ivory Coast, Hassan samoh daga Thailand, Abdulrahman Ashraf daga Masar, su ne a matsayi na farko.

An bayar da kyautar kudade dirham dubu 250 ga wadanda suka zo na daya, dubu 150 ga na biyu, dubu 100 ga na uku, haka nan kuma an bayar da dubu 50 ga na hudu har zuwa na goma, kamar yadda kuma aka bayar da kyautar kudade har Dirham dubu 30 ga duk wanda ya halarci wanan gasa ko da bai ci ba.

Wannan gasa dai ta gudana ne a babban dakin harkokin kasuwanci na Dubai, kuma Muhamamd Behzadfar daga kasar Iran shi ne ya wakilci kasar, amma saboda wasu dalilai daga bangaren alkalancin da aka yi a gasar bai samu tsallakewa zuwa ga wani mataki, ko da a mataki na mutane 10 da suka fi nuna kwazo bai samu shiga ba, duk kuwa da cewa ya amsa tambayoyi yadda ya kamata.

3325795

Abubuwan Da Ya Shafa: dubai
captcha