Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alwifaq cewa, jam’iyyar ta bayyana cewa sake kame Ibrahim Sharif daya cikin shugabannin kungiyar Wa’ad da mahukuntan kasar suka yi, ya kara tabbatar da cewa mahukuntan kasar ba a shirye suke su yi duk wani sauyi ba a cikin harkokin mulki da siyasa ba.
Jami’ar ta Alwifaq ta ce tana ira ga muhuntan kasar da su gagauta sakin Ibrahim Sharif ba tare da wani bata lokaci ba, kuma ci gaba da rike zai zama wani babban lafi da zai kara dagula lamurra ta fuskoki da dama akasar.
Bayan ‘yan kawanaki da sakin Ibrahim Sharif, mahukuntan kasar Bahrain sun sake kama shi bisa hujjar cewa ya saba kaidoji da dokokin kasar, bayan da ya kwashe ksan shekaru biyar a tsare bidsa hujjoji marassa kan gado.
Jam’iyyar Alwifaq ta ce masarautar mulkin mulukiya ta kasar tana tafka babban kure a cikin ayyukan da ke yin a yunkurin murkushe duk wani wanda ya nemi da a gudanar da gyara a cikin lamarin mulkin kasar, ta hanyar kamu da dauri da cin zarafi.
3327187